Nigeria ta kaddamar da sabuwar N100

Hakkin mallakar hoto Nigeria State House
Image caption An kaddamar da sabuwar N100 ne domin cikar yankin arewa da na kudancin kasar shekara dari da hadewa.

Nigeria ta kaddamar da sabuwar N100 domin cikar yankin arewa da na kudancin kasar shekara dari da hadewa.

Shugaban Babban bankin kasar, Godwin Emefiele ne ya kaddamar da takardar kudin a wajen taron majalisar zartarwa a fadar shugaban kasar da ke Abuja.

Sai dai za a fara amfani da takardar kudin ne ranar 19 ga watan Disamba mai zuwa.

Kazalika, za a ci gaba da amfani da takardar kudin N100 da dama ake amfani da ita dama.

Karin bayani