'Yan gudun hijira na kwana a kasuwanni

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Fiye da 'yan gudun hijirar Najeriya dubu 100 ne ke samun mafaka a kasashe makwabta

Rahotanni daga Kamaru na cewa mawuyacin halin da 'yan gudun hijrar Nigeria ke ciki yasa wasu ke kwana a kasuwanni da tashar mota.

A baya-bayan nan dai wasu 'yan gudun hijira daga Mubi na jihar Adamawa da ba a san adadinsu ba ne suka shiga garin Doumo na jamhuriyar Kamaru.

Kuma bayanai na nuna cewa suna fuskantar matsaloli na halin rayuwa kamar rashin samun muhalli da kuma wasu ababan more rayuwa.

Wani dan gudun hijirar Najeriya da suka tsere daga Gamboru a jihar Borno kuma suke Fotokol a kasar Kamaru ya gaya wa BBC cewa "Ko likkafani babu idan mutum ya mutu."