'Yan gudun hijira 13, 000 sun gudu Kamaru

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hukumar ta ce akasarin 'yan gudun hijirar mata ne da kananan yara

Hukumar kula da 'yan gudun hijra ta duniya ta ce 'yan gudun hijira daga Nigeria su 13,000 ne suka tsallaka zuwa Kamaru a watan Oktoba kawai.

Hukumar ta ce jami'an gwamnatin Kamaru sun shaida mata cewa akasarin 'yan gudun hijirar sun gudu Kamaru ne bayan 'yan kungiyar Boko Haram sun kama garin Mubi na jihar Adamawa.

Yawancin su sun shiga garuruwan Guider da Gashiga da ke arewaci da kuma garuruwan Bourha, Mogode da Boukoula da ke arewa mai nisa ta Kamaru.

Sai dai hukumomin Kamarun sun ce yawancin 'yan gudun hijirar sun koma Nigeria, kuma mafi yawansu suna zaune ne yanzu a birnin Yola na jihar ta Adamawa.

Hukumar da ke kula da 'yan gudun hijirar ta kara da cewa akasarin 'yan gudun hijirar mata ne da kananan yara, kuma sun tsere zuwa Kamaru ne a kafa, inda suka shiga mummunan yanayi.

Karin bayani