2015: Buba Galadima ya raba gari da Buhari

Image caption An fara yakin neman zabe a Nigeria, amma a wannan karon Buba Galadima ya sauya Ubangida

Wani jigo a jam'iyyar adawa ta APC, Injiniya Buba Galadima ya ce ba ya tare da Janar Muhammadu Buhari a zaben 2015 da ke tafe a kasar.

A wata hira da BBC Buba Galadima ya ce ya raba gari da janar Buhari ne saboda a shekarar 2011 janar din ya shaida musu cewa ba zai sake tsaya wa takara ba.

Inda ya kara da cewa yana bin akidar janar na mai magana daya, kuma tun da bai kira shi ya shaida masa zai tsaya takara ba a zaben da ke tafe, a iya saninsa bai fadi zai yi takara ba.

A watan Oktoba da ya wuce ne dai Janar Buhari ya kaddamar da aniyarsa ta neman zama dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar APC a zaben 2015.