Kungiyar likitoci za ta yi gwajin magajin Ebola

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mutane fiye da 5000 ne suka mutu sakamakon cutar Ebola

Kungiyar agajin likitoci ta Medicines Sans Frontiers, MSF, ta ce za ta jagoranci wasu gwaje-gwaje da za a yi a wasu asibitoci a yammacin Afrika, domin neman maganin cutar Ebola.

A cewar kungiyar, za ta yi amfani da wasu magungunan yaki da kwayoyin cututtuka guda biyu da kuma wani bangaren jinin wadanda suka warke daga cutar ta Ebola.

MSF ta kuma kara da cewa za ta gudanar da gwaje-gwajen ne domin ganin ko akwai yuwuwar a inganta lafiyar wadanda suka kamu da cutar.

Idan dai har wadannan gwaje-gwajen da za a yi makonni biyu ana yi ya yi tasiri, ana sa ran za a samar da magunguna ga masu fama da cutar.