An kama likitan da ya yi tiyatar juya mahaifa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan sanda sun ce likitan zai gurfana a gaban kuliya

'Yan sanda a India sun kama likitan da ya yi wa wasu mata tiyatar juya mahaifa, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar wasunsu.

Mata goma sha biyar ne suka mutu sanadiyar matsalar da aka samu lokacin yin tiyatar.

An kwanatar da matan da dama a asibiti a jihar Chhattisgarh, bayan sun rika yin amai da zubar da jini.

Har yanzu dai likitoci na duba lafiyar fiye da mata casa'in wadanda aka yi wa wannan tiyata.

Babban jami'in 'yan sandan yankin ya ce likitan mai suna, R.K.Gupta, zai gurfana a gaban kuliya ranar Alhamis.

Karin bayani