An kwato Mubi daga hannun Boko Haram

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana caccakar dakarun Nigeria saboda Boko Haram

Rahotanni daga Nigeria na cewa an sake kwace garin Mubi na jihar Adamawa daga hannun 'yan kungiyar Boko Haram.

Bayanai sun nuna cewar mafarauta da 'yan civilian JTF tare da hadin gwiwar jami'an tsaro ne suka samu nasarar kwace garin na Mubi.

A cikin watan Okotoba ne 'yan Boko Haram suka kwace garin Mubi inda suka fatattaki sojoji daga garin, lamarin da ya tilastawa dubbai mutane yin hijira.

A farkon wannan watanne 'yan Boko Haram sun canzawa Mubi suna ya koma 'Madinatul Islam' inda suka kafa tutocinsu.

Garin Mubi shi ne na mafi biyu a girma a jihar ta Adamawa.