Ukraine: Rasha tana ruruta rikici a boye

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Samantha Power ta ce Rasha tana zagon kasa a boye akan zaman lafiya a Ukraine

Amurka ta zargi Rasha da yin makarkashiya don kawo tarnaki ga yarjejeniyar da aka cimma a watan Satumba ta tabbatar da zaman lafiya a Ukraine.

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Samantha Power ta shaidawa kwamitin tsaro na Majalisar cewa Moscow ta na fadin zaman lafiya a baka ne, amma tana ruruta wutar rikicin ta wata hanya.

Samantha Power ta ce taron na baya bayan nan akan rikicin Ukraine shi ne karo na 26, kuma Rasha ta sha daukan al'kawari na kawo karshen rikicin amma akarshe, bata cikawa.

Zargin da Amurka tayi wa Rashan ya zo ne bayan kungiyar tsaro ta NATO ta yi gargadin cewa Moscow ta na barazana ga 'yar jaririyar yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a gabashin Ukraine, ta hanyar girke dakarunta a yankin.

Sai dai a jawabinsa a wajen taron, mataimakin jakadan Rasha a Majalisar Dinkin Duniya, Alexander Pankin ya yi watsi da zargin, inda yace farfaganda ce kawai.