Tambuwal ya karbi fom din takara a APC

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Tambuwal da Kwankwaso na hammaya da juna a APC

Shugaban Majalisar Wakilan Nigeria, Aminu Waziri Tambuwal ya karbi takardar neman izinin tsayawa takarar shugabancin kasar a karkashin inuwar jam'iyyar APC.

Kakakin shugaban majalisar ya tabbatarwa da BBC cewar abokai da magoya bayansa na siyasa ne suka saye takardar neman takarar shugabancin kasar a madadin Tambuwal din.

A karshen watan Oktoba ne Tambuwal ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC, abinda ya sa gwamnati ta janye masu jami'an tsaron da ke kare lafiyarsa.

Tambuwal ya zama mutum na biyar da ya nuna sha'awar neman tsayawa takarar shugabancin Nigeria a inuwar jam'iyyar APC.

Sauran 'yan takarar su ne Janar Muhammadu Buhari da Alhaji Atiku Abubakar da Injiniya Rabiu Kwankwaso da kuma Mr Sam Nda Isaiah.

Duk wanda ya lashe zaben fitar da gwani tsakanin 'yan takarar na APC, zai hadu da Shugaba Goodluck Jonathan wanda jam'iyyar PDP ta tsayar babu hammaya a zaben shugaban kasa na 2015.