YouTube zai fara cajin wasu mutane kudi

Hakkin mallakar hoto spotify
Image caption Masu amfani da Youtube za su iya sauke wakoki don kallo a kowanne lokaci ta Music Key

Shafin Youtube mallakin kamfanin Google zai fara wani tsari da zai rika cajin masu amfani da shi kudi domin basu damar kallon wakokin bidiyo a shafin batare da suna ganin tallace-tallace ba.

Tsarin zai kuma ba masu amfani da Youtube damar sauke hotunan bidiyon a kan wayoyin salularsu domin kallo ko babu intanet.

Sabon tsarin mai suna "Music Key" wanda masu bukata zasu rika biyan fam 9.99 a kowanne wata, zai kuma ba jama'a damar sauke wakoki akan wayoyinsu daga runbum "Google Play All Access".

Tsarin na Music Key zai zamo kishiya ga Spotify, da Rdio da Beats Music da sauran hanyoyin sauraron wakoki zalla a intanet.

Shafin na Youtube ya yi jinkirin kaddamar da sabon tsarin ne saboda wata takaddama, amma kamfanin Google ya ce yanzu ya rattaba hannu a wata yarjejeniya da daruruwan mawaka na duniya da suka amince da shi.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Google ya sanya wakokin Billy Bragg a cikin tsarin Music Key

Hakan ya ba Google damar sanya wakoki da suka hada da na Billy Bragg.

Tashar yada labarai ta BBC ta gano cewa bisa yarjejeniyar da Google ya kulla da mawaka, mawakan da akafi kallo ko sauraron wakokinsu za su fi samun kaso na kudin da Youtube zai rika karba daga masu amfani da shi.

Wayoyi masu amfani da manhajar Android ne zasu fara samun damar sauke wakoki ta Music Key, daga nan kuma sai wayoyin Apples, amma banda kwamfutoci.

Sabon tsarin zai bai wa mutane damar cigaba da sauraron wakoki a yayin da suke yin wasu harkokin da wayoyinsu.

Wadanda basu da sha'awar biyan kudi zasu iya sauraron wakokin mawaka daga farko zuwa karshe, amma baza su iya kallon wakokin ta hoton bidiyo ba.