Wannan baraka ce a APC ?

Janar Muhammadu Buhari Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Janar Muhammadu Buhari

A Nigeria bisa ga dukkan alamu ana samun baraka tsakanin wasu 'ya'yan babbar jam'iyyar adawa ta APC game da batun tsayawa takarar kujerar shugaban kasa na Janar Muhammadu Buhari a zaben shekara ta 2015.

Hakan dai ta fito fili ne bayan da wasu magoya bayan Janar Muhammadu Buhari suka maida martani dangane da kalaman da wani jigo a jam'iyyar kuma na hannun damar Janar Buhari, Injiniya Buba Galadima ya yi, wanda yace ba ya tare da Janar Buhari a zaben shekara ta 2015 saboda kalaman da Buhari ya yi bayan zaben shekara ta 2011 cewa ba zai sake yin takara ba, don haka a cewar sa bai dace ya sauya matsayi ba.

To, sai dai a hirar su da BBC, wani na hannun damar Janar Buhari Honorable Faruk Adamu Aliyu ya ce kalaman da Buba Galadima ya yi sun ba su mamaki matuka.

Faruk Aliyun yace, babu baraka a jam'iyyar APC, duk wanda ya yi nasara a zabe za su rufa masa baya, amma dai kamata ya yi Buba Galadima wanda yace ba shi da shamaki da Janar Buhari, ya je ya nuna masa kuskuren da ya yi.

Karin bayani