Za a nada shugaban wucin gadi a B/Faso

Hakkin mallakar hoto

Shugaban mulkin sojin Burkina Faso ya baiwa kungiyoyin masu fafutuka wa'adin gobe lahadi da su fidda jerin sunayen wadanda za a zabi shugaban kasar na wucin gadi a tsakaninsu.

Laftana Kanar Izak Zida ya amince ne da wani shirin kungiyoyin farar-hulan kasar na mai da kasar ga turbar demokuradiyya.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne shugabannin jam'iyyun adawa da kuma kungiyoyin farar hula suka cimma yarjejeniyar amincewa da gwamnatin wucin-gadi, wadda za ta mulki kasar zuwa badi.

Sai masana na ganin cewa yakamata jama'a ne yakamata su zabi shigaban wucin gadin kasar ba shugaban mulkin sojin kasar ba.

Dr Jibrin Ibrahim shi ne shugaban cibiyar raya demokradiyya ta Centre for Democracy and Development da ke Abuja,Ya shaidawa BBC cewa yakamata kungiyoyin farar hular sun fidda mutum guda da Laftana Zidan zai amince da shi.

A watan jiya ne aka hambaradda shugaba Blaise Campore wanda yayi 27 yana mulkin kasar a wani bore.