Za a kafa gwamnatin wucin gadi a Burkina Faso

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Za a yi zaben shugaban kasa a karshen shekara ta 2015 a Burkina Faso

An cimma yarjejeniya kan sigar da za a bi don kafa gwamnatin wucin gadi a Burkina Faso, wadda za ta jagoranci kasar zuwa lokacin da za a yi zabe a badi.

Sojoji da jam'iyyun adawa da kungiyoyin fararen hula da kuma shugabanin addinai ne suka hadu suka amince da yadda za nada shugaban rikon kwarya da majlisar dokoki.

Makonni biyu kenan da sojoji suka hambarar da gwamnatin Blaise Compaore wadda ta shafe shekaru 27 tana mulki a kasar.

Tun da fari dai hukumar ba da lamuni ta duniya, IMF ta ce ba zata sabunta shirin bada tallafi na miliyoyin daloli ga kasar ba, har sai an kafa gwamnatin da kasashen duniya suka amince da ita.