Jirgin soji ya hallaka mutane uku a Yola

Hakkin mallakar hoto Adamawa Resident
Image caption Nigeria na fuskantar kalubalen tsaro

Rundunar sojin Nigeria ta ce dakarunta uku sun mutu a cikin wani jirgin sama mai saukar angulu da ya fadi a Girei na jihar Adamawa.

Jirgin saman shi ne jirgin sojin Nigeria na biyu cikin kwanaki uku da ya yi hadari a jihar Adamawa inda ake yaki tsakanin dakarun kasar da 'yan kungiyar Boko Haram.

Wasu mazauna garin Girei sun shaidawa BBC cewa lamarin ya faru ne lokacin da wasu jirage biyu ke kokarin wucewa kuma ana zaton jirgin da ya fado na dauke da makamai.

Dalibai a jami'ar Modibbo Adama da ke Yola sun shaidawa BBC cewar sun ji kara mai karfi, abinda ya jefasu cikin firgici a kan ko 'yan Boko Haram ne suka kai musu hari.

Hakan na zuwa ne kwana guda bayan da maharba da 'yan sintiri suka kwato garin Mubi daga hannun 'yan Boko Haram.