Kungiyar IS ta kashe Peter Kassig

Hakkin mallakar hoto AP

Kungiyar masu jihadi ta sanya wani hoton bidiyo a internet da ke nuna yadda mayakanta suka halaka wani dan agaji Ba'amurke mai suna Abdul-Rahman Kassig, wanda aka fi sani da Peter Kassig, wanda aka sace a kasar Syria, bara.

Bidiyon mai tsawon minti 15 da aka wallafa a internet da safiyar yau, na kunshe da hotuna mafi muni da Kungiyar IS din mai fafutukar kafa daular muslunci ta fitar.

Ya nuno wani mutum da ya rufe fuskarsa yana tsaye a kan wani kai da ya ce na Mista Kassig ne.

Amurka ta ce tana kokarin tabbatar da sahihancin bidiyon wanda ya kuma nuna yadda aka kashe wasu dakarun Syria da dama.

Iyalan sa da ke jihar Indiana ta Amurka sun ce suna jiran tabbacin labarin mutuwar dan nasu daga gwamnati, kuma a yanzu babu wani abin da za su ce illa a bar su su yi jimamin mutuwarsa ba tare da wata katsalandan ba.

Firayim Ministan Birtaniya David Cameron ya ce ya kadu matuka da kisan gillar da aka yi wa Mista Kassig.

Mista Cameron ya kuma ce kungiyar IS ta sake tabka wani aikin rashin hankali.

A bara ne IS ta kama Peter Kassig wanda ya je aikin agaji a Syria.

Ya karbi Musulunci daga baya kuma har ya sauya sunansa zuwa AbdulRahman Kassig.

Kisan nasa dai ya nuna cewa kungiyar IS din ba ta da niyyar yin sassauci a kashe-kashen da take yi.