Bom ya halaka mutane shida a Kano

Image caption Jihar Kano ta yi fama da matsalar dana bom a baya

A Najeriya, rundunar 'yan sanda a jihar Kano dake arewacin kasar ta ce wani dan kunar bakin wake da shiga cikin gidan mai da mota kirar Sienna ya tada bom, inda ya kashe kanshi da karin wasu.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Magaji Musa ya ce mutane shida ne suka mutu sakamakon harin, kuma uku daga cikinsu jami'an 'yan sanda ne.

Mutane da dama sun samu raunuka sakamakon fashewar wadda ta faru a kusa da wani gidan mai na NNPC lokacin da wata motar dakon mai ke sauke kaya.

Bayanai sun nuna cewa wurin da aka samu fashewar, matattarar jami'an tsaro ce, sannan kuma mutane na gudanar da hada hada a wajen.

Babu wani ko wata kungiya data dauki al'hakin kai harin, amma a baya, kungiyar Boko Haram ta sha kai irin wannan hari a jihar.