An dage dokar ta-baci kan Ebola a Liberia

Hakkin mallakar hoto ap
Image caption A watan Agustan da ya wuce ne aka sanya dokar ta baci don shawo kan yaduwar cutar Ebola a Liberia

Shugabar kasar Liberia, Ellen Johnson Sirleaf , ta dage dokar ta-baci da ta sanya don shawo kan cutar Ebola da ta addabi kasar.

Sirleaf ta dage dokar ne saboda masu kamuwa da cutar sun ragu, amma ta ce hakan ba wai yana nufin an daina yaki da bazuwar cutar a kasar ba.

A wani jawabi da ta yi wa 'yan kasar, shugabar ta ce za a rage tsawon dokar hana fita da daddare, haka kuma za a iya cin kasuwannin mako-mako a kasar.

Ta kara da cewa ana shirye-shiryen sake bude makarantu a kasar.