Boko Haram: Yara 6000 na neman mafaka

Hakkin mallakar hoto AFP

Hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeria, wato NEMA ta ce akwai yara kanana sama da 6000 na sansanonin da aka tsugunnar da wadanda rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu.

Cikin yaran har da wandanda ba a san inda iyayensu suke ba.

Galibin yaran na sansanin Yola ne dake Jihar Adamawa.

Kakakin hukumar ta NEMA, Malam Sani Datti ya shaidawa BBC cewa suna taimakawa yaran, kuma gwamnati zata dauki nauyin karatun su.

Zata karantar da yaran ne a cewar Malam Sani Datti, a bisa sabon tsarin makarantun da aka samar masu da tsaro

Yanzu haka dai miliyoyin jama'a ne rikicin na Boko Haram ya daidaita.

Wasu daga cikin masu gudun hijirar na zaune a wasu kasashe kamar su Kamaru, da Chadi, da Nijar