'Yan bindiga sun sace shanu 1000

Image caption An gano shanu 300 daga cikin dubu daya da a ka sace

A Najeriya, rahotanni daga jihar Filato dake yankin tsakiyar kasar sun ce wasu 'yan bindiga sun kai hari kan Fulani makiyaya a karamar hukumar Kanke, inda suka kwace shanu kimanin dubu daya.

Rahotannin sun ce lamarin ya faru ne kusa da kauyen Lanchi a kan iyakar yankin Langtang, kuma 'yan bindigar sun kashe mutum daya daga cikin makiyayan.

Makiyayan da suka bi sawun 'yan bingigar sun gano shanu kimanin 300 wadanda suka fandare wa barayin.

Rundunar 'yan sandan jihar Filato ta ce za ta yi bincike don tabbatar da ko harin ya auku, amma kungiyar Filani ta Miyetti Allah a jihar ta tabbatar da faruwar lamarin.

Jihar ta Filato dai ta dade tana fama da tashe-tashen hankula masu nasaba da kabilanci da addini da kuma matsalar satar shanu.