Rasha zata yi wa Wikipedia kishiya

Hakkin mallakar hoto Wikipedia
Image caption Bincike ya nuna babu isassun bayanai a game da Rasha a Wikipedia

Dakin karatu na fadar shugaban kasar Rasha ya ce gwamnatin kasar ta na shirin samar da shafin tattara bayanai na ko-mai-da-ruwanka a intanet, wanda zai zama kishiya ga shafin Wikipedia.

A cikin wata sanarwa, dakin karatun ya ce manufar samar da sabon shafin ita ce a samar da isassun bayanai a game da Rasha da suka fi wadanda ke cikin shafin Wikipedia.

Bincike ya nuna cewa babu isassun bayanan da za a iya dogaro dasu a kan yankunan Rasha, da tarihin kasar da sauran harkokinta a cikin shafin Wikipedia.

Dakin karatun na fadar shugaban kasar Rasha ya ce an tattara litattafai da sauran takardun bayanai dubu hamsin da nufin bada bayanai na gaskiya a game da Rasha.

Sai dai akwai babban aiki a gaban sabon shafin na ko-mai-da-ruwanka, yayin da Wikipedia shi ne na shida cikin shafukan intanet da mutane suka fi amfani da su a duniya.

Wannan sabon shiri ya zo ne a dai dai lokacin da gwamnatin Kremlin ke kara kaimi wajen sa ido da kula da al'amuran intanet.

A watan Agusta, kasar ta kafa wasu dokoki da suka tilasta wa mutane masu tafiyar da shafukan intanet wadanda mutane fiye da dubu uku ke ziyartar su a kowacce rana yin rijista da hukumar kula da kafafen yada labarai.

A watan Maris, gwamnatin kasar ta rufe wasu shafukan intanet na wasu 'yan adawa, masu sukar shugaba Vladimir Putin.