'An samu nasara a yaki da cutar Polio'

Hakkin mallakar hoto AFP

Cibiyar da ke yaki da cututtuka ta Amurka ta bayyana cewa an samu gagarumar nasarar wajen yaki da cutar shan-Inna a duniya.

Kwararru sun ce an ci nasarar kawar da nau'i na biyu na kwayar cutar sakamakon allurar da ake yi ta riga-kafi.

Sai dai sun ce za a dauki nan da karshen wata shekara kafin a kawar da nau'i uku na cutar a duniya.

Kasashen Najeriya da Pakistan dai su ne har yanzu ba su kai ga kawar da cutar ta shan inna ba, sakamakon ikirarin da suke yi cewa suna fuskantar matsala wajen shiga yankunansu da ke fama da rigingimu don yin allurar riga-kafin cutar.

Amma duk da haka, kwararru sun ce an samu nasara. Mr Oliver Rosenbua, jami'i ne na Hukumar Lafiya ta duniya: