An samu wasu da laifin cin naman mutun

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan sanda sun gano sassan jikunan matan da a ka kashe

A kasar Brazil, an yanke wa wasu mutane uku a jihar Pernambuco dake arewa maso gabashin kasar hukuncin dauri mai tsawo a gidan kurkuku, saboda kisan kai da kuma cin naman mutanen da suka kashe.

Jorge Silveira, da matarsa da kuma wata buduruwarsa, sun yaudari wasu mata uku da cewa zasu sama musu aikin yi, kafin su kashe su, tare da cin naman wasu sassan jikunansu.

An yanke wa Silveira hukuncin daurin shekaru 23, bisa kasancewa jagora a aikata laifin.

Iyalin Mr. Jorge sun yi amfani da naman sassan jikunan matan da a ka kashe, wajen yin wani abinci mai kama da meatpie.

Akalla mutane dubu hamsin ne a ke kashewa a Brazil a kowace shekara, sai dai kadan ne daga ciki a ke wa irin wannan kisar gilla.