Ku daina tsoron Boko Haram - Sarkin Kano

Image caption Mai Martaba, Muhammadu Sanusi na biyu

Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi II ya bukaci 'yan Nigeria su tashi su kare kansu daga hare-haren 'yan kungiyar Boko Haram.

Sarkin ya bayyana haka ne a lokacin taron addu'o'i na mako mako a Kano, inda ya ce kada mutane su za ci cewa sojoji kadai za su iya kare su.

Ya bukaci malaman addinai da su ci gaba da fadakar da jama'a muhimmancin jaruntaka da juriya, inda ya ce addu'a kadai ba za ta fitar da jama'a daga halin da suke ciki ba sai sun tashi tsaye.

Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi II ya ce kada mutane su karaya ganin yadda mayakan Boko Haram ke kwace garuruwa, inda ya ce tilas a al'umma su nuna juriya tare da sadaukar da rayukar su don kare iyalai da dukiyoyin su.