Yaro ya zama kwararren kwamfuta

Hakkin mallakar hoto AYAN QURESHI
Image caption Ayan yana shafe kusan sa'oi biyu a kullum kan koyon ayyukan kwamfuta

Wani yaro dan shekara biyar ya zama kwararren masanin kwamfuta mafi karancin shekaru a duniya

Ayan Qureshi wanda ya fito daga Coventry ta Ingila ya samu nasara ne a jarrabawar kamfanin Microsoft tun yana shekara biyar.

Ayan, wanda yanzu ya kai shekara shida, wanda babansa masanin kwamfuta ne, ya hada dandalinsa na kwamfuta(network) a gida.

Yaron ya sheda wa BBC cewa, jarrabawar ta yi wuya, amma kuma ya ji dadinta.

Mahaifin yaron , ya soma koya masa kwamfuta, tun yana shekara uku.

Inda ya rika ba shi dama yana wasa da tsofaffin kwamfutocinsa.

Mahaifin ya ce barin yaro mai shekarunsa ya yawaita amfani da kwamfuta hadari.

To amma shi kuma Ayan, hakan ya kasance daban a wurinsa.

Hakkin mallakar hoto v

Lokacin da ya je yin jarrabarawar, masu kula da jarrabawar, sun nuna damuwa akan shekarunsa.

Amma kuma mahaifinsa ya tabbatar musu cewa ba shi da matsala.

A shekara ta 2009 ne iyayen Ayan suka dawo Ingila da zama daga Pakistan.

Ayan ya ce burinsa shi ne ya kafa cibiyar fasahar sadarwa ta zamani a Birtania kamar ta Amurka, Silicon Valley, wadda zai sanya wa suna E-Valley.