Matasa sun yi tur da 'yan siyasar Bauchi

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Matasan sun kona hotunan 'yan siyasa

Matasa a garin Azare na jihar bauchi da ke Nigeria sun dora alhakin tabarbarewar tsaron jihar kan 'yan siyasa, suna masu yin Allah-wadai da halayyarsu.

Matasan -- wadanda suka yi zanga-zanga ranar Lahadi bayan wani harin bam da aka kai a Azare ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da goma --- sun yi zargin cewa 'yan siyasar na da hannu a hare-haren da ke faruwa a jihar.

Sun kona hotuna da allunan takara na jam'iyyun kasar daban-daban ba tare da nuna bambanci ba, domin nuna fushinsu ga 'yan siyasar.

Harin da wasu da ake zargi 'yan Boko Haram ne suka kai a garin na Azare shi ne na biyu a cikin makonni biyu.