Boko Haram: Za a kara tsawaita dokar ta-baci

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Abubakar Shekau ya soma wa'azi a bayyane a cikin masallaci

Majalisar tsaro ta Nigeria ta amince a kara tsawaita dokar ta-baci a jihohin Adamawa da Borno da kuma Yobe.

Ministan Shari'a na Nigeria, Mohammed Bello Adoke ne ya bayyana matsayin majalisar bayan kamalla taron a fadar shugaban kasar da ke Abuja.

Mr Adoke ya ce shugaba Jonathan zai aika bukatar neman izinin majalisar dokokin kasar domin amincewa da karin wa'adin dokar ta-bacin.

A bisa tsari, a ranar 20 ga watan Nuwamba ne wa'adin dokar ta-bacin da gwamnati ta kafa zai kare.

Tun a watan Mayun 2013 ne Mr Jonathan ya kafa dokar ta-baci a jihohin na arewa maso gabashin Nigeria.

Masu sharhi na ganin cewar dokar ta-bacin ba ta yi tasiri ba tunda aka kafa ta, saboda yadda 'yan Boko Haram ke tsananta kai hare-hare.

A yanzu haka 'yan Boko Haram na iko da garuruwa da dama a jihohin Borno da Yobe da kum Adamawa.