An bude makarantun gwamnati a Borno

Image caption Gwamna Kashim Shettima na Borno

Gwamnatin jihar Borno ta bude wasu daga cikin makarantun na firamare da na sakandare da ke fadin jihar bayan da aka rufe su a cikin watan Maris na wannan shekarar.

Gwamnatin jihar ta ce an rufe makarantun a waccan lokacin ne saboda kalubalen tsaro da ke addabar jihar.

Kungiyar Boko Haram wacce ke kokarin kafa daular Musulunci ta haramta karatun Boko.

A watannin baya, gwamnan jihar Borno, Alhaji Kashim Shettima, ya ce an kashe malaman makaranta 176 tare da kona makarantu fiye da 900 tun lokacin da aka soma rikicin Boko Haram a shekara ta 2011.

A farkon wannan watan 'yan Boko Haram sun hallaka dalibai kusan 50 a Potiskum da ke jihar Yobe mai makwabtaka da jihar Borno.

'Yan Boko Haram na adawa da karatun Boko abin da ya sa kungiyar ta sace dalibai 'yan mata fiye da 200 a cikin watan Afrilu a makarantarsu da ke Chibok a jihar Borno.