'An tsige kakakin majalisar Ekiti'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Rahotanni sun ce yanzu haka 'yan sanda suna can suna gadin ginin majalisar

'Yan majalisar dokokin jihar Ekiti bakwai da ke goyon bayan jam'iyyar PDP, sun ce sun tsige kakakin majalisar dokokin jihar, Honourable Adewale Omirin na jam'iyyar APC.

'Yan majalisar sun zabi Honourable Olugbemi a matsayin sabon kakakin majalisar dokokin.

Rahotanni daga jihar Ekiti sun rawaito cewa 'yan majalisar dokokin bakwai sun rinjayi sauran 'yan majalisar dokokin na jam'iyyar APC 19.

Rahotannin sun ce 'yan majalisar sun dauki matakin ne bayan samun kariya daga jami'an 'yan sanda sai dai rundunar 'yan sandan jihar ta musanta hakan.

Yanzu haka dai jami'an 'yan sanda na can suna ci gaba da kare majalisar domin kaucewar tashin hankali.

Jihar Ekiti dai na fama da dambarwar siyasa a wani yanayi da ake zaman doya da man ja a tsakanin jam'iyyar PDP da APC .

Karin bayani