Michel Kafando ne shugaban Burkina Faso

Michel Kafando Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption An haramtawa Mr Kafando tsayawa takara a zabe mai zuwa.

Hukumomi a kasar Burkina Faso sun sanar da sunan Ministan harkokin wajen kasar Michel Kafando a matsayin shugaban rikon kwarya, hakan ya biyo bayan rattaba hannun da sojoji suka yi da shugabannin fararen hula domin kafa gwamnatin da za ta rike kasar na shekara guda kafin gudanar da zabe.

An dai zabe shi ne a daidai lokacin da wa'adin da kungiyar Tarayyar Afurka ta bada domin gujewa kakabawa kasar takunkumin tattalin arziki.

Mr Kafando na daga cikin mutane hudun da aka bada sunayensu da suka hada da 'yan jarida biyu, da kuma malamin jami'a.

Babban kalubalen da ke gabanshi shi ne ya samar da Prime Ministan da zai jagoranci kasar, Sai dai za a haramtawa Mr Kafando tsayawa takarar shugabancin kasar a zabe mai zuwa.

Sojojin Burkina Faso sun jagoranci kasar na takaitaccen lokaci bayan da juyin-juya hali a kasar ya tilastawa shugaba Blaise Compaore yin murabus tare da ficewa daga cikin ta.