An ayyana dokar ta baci a Missouri

Masu zanga-zanga a lokacin da aka kashe Micheal Brown Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Bakaken fata dai na fuskantar barazana iri-iri daga jami'an 'yan sanda a Amurka.

An ayyana dokar ta baci ta wata guda a jihar Missouri ta Amurka, gabannin yanke hukuncin ko za a tuhumi dan sandan nan farar fata da ya harbe har lahira wani matashi bakar fata Micheal Brown a watan Agusta da gabata wanda baya dauke da makami.

Bayan rattaba hannu kan dokar ta bacin, gwamnan jihar Jay Nixon ya bukaci karin jami'an tsaro da su tallafawa 'yan sanda domin tabbbatar da zaman lafiya a garin Ferguson da kuma yankin St Lious idan masu taimakawa alkali yanke hukunci sun sanar da hukuncin da suka yan ke.

Ta yiwu ma a kara tsawaita dokar idan bukar hakan ta taso. a watan Agustan da ya gabata ne aka harbe matashin, abinda ya janyo zanga-zangar kin amincewa da bakaken fata suka jagoranta a kasar.

Haka kuma lamarin ya janyo zazzafar muhawara kan dangantakar da ke tsakanin 'yan sanda bakaken fata a Amurka.