An kashe mutane biyar a Nasarawa

Hakkin mallakar hoto Nigeria Police
Image caption Sufeto Janar na 'yan sandan Nigeria, Sulaiman Abba

'Yan sanda a jihar Nasarawa sun tabbatar da mutuwar mutane 5 sakamakon rikicin da ya barke tsakanin Fulani da kuma 'yan kungiyar Ombatse a kauyen Alakiyo.

Haka kuma mutane da dama sun jikkata a yayinda aka kona ababan hawa sakamakon lamarin.

Wannan fada dai ya kuma fantsama daga kauyen Alakiyo zuwa wani gari da ake kira Shabu wanda keda nisan kilomita biyu daga Lafiya babban birnin jihar.

'Yan sandan sun ce yanzu haka hankali ya soma kwanciya kuma an tsaurara jami'an tsaro a fadin jihar.

Bayanai sun nuna cewa makarantu a garin Lafiya sun kasance a rufe a ranar Litinin saboda fargaba.

An jima ana fada i tsakanin Fulani da kuma 'yan kungiyar Ombatsen.