Murar tsuntsaye ta sake bulla a Neitheland

Kwararru na bincikar lafiyar wasu kaji Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ba wannan ne karo na farko da ake samun bullowar murar tsuntsaye ba a kasar ta Neitherlands

Hukumar kungiyar kasashen turai na gab da sanar da sabbin matakai domin magance ballewar murar tsutsaye mai hadarin gaske da ta balle a wata gona a kasar Neitherlands.

Kakakin hukumar ya yi gargadin cewa ballewar annobar ka iya yin illa ga lafiyar bil'adama.

Tuni dai Neitherland ta bada umarnin umarnin kashe kashi dubu hamsin a gidan gonar da annobar ta bullo da ke garin Hekendorp.

An kuma ayyana dokar haramta shiga ko fitar da kaji da kwai daga cikin kasar.