Mata za su zama limamai a cocin Ingila

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugabannin Cocin Ingila

Cocin Ingila ya kawo karshen wata al'adar shekaru aru -aru ta hanyar amincewa da wata dokar da za ta bayar da dama a nada mata a matsayin limamai a karon farko.

Sauyin dokar cocin ya samu karbuwa da gagarumin rinjaye a babban taron shugabannin cocin a birnin London.

Hakan dai ya faru ne shekaru 20 bayan da a karon farko cocin na Ingila ya nada mata a matsayin malamansa.

Kuma kafin yanzu ba su samu damar daukar kaiwa mutamin limamai watau mukami mafi girma a cocin.

Wani kokari na bullo da mukamin bishop - bishop mata bai samu nasara shekaru biyu da suka wuce.