'Akwai bayi miliyan 36 a duniya'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption India ta fi kowacce kasa a duniya yawan bayi

Wani sabon nazari na nuna cewa akwai kusan mutane miliyan talatin da shida a duniya da ke cikin kangin bauta.

Kungiyar kididdige ayyukan bauta ta duniya, Global Slavery Index, ta ce India ce ta fi kowace kasa a duniya yawan bayi, wadanda aka kiyasta sun kai sama da miliyan sha hudu, inda kasar China ke bi mata, sai kasar Pakistan wacce ke ta uku.

Ita kuma kasar Mauritania ita ce wadda aka fi samun bayi cikin kason al'umarta, domin kuwa kashi hudu cikin dari na al'ummar kasar na zaune ne a matsayin bayi.

An kasafta bayin ne a matsayin mutanen da ake tilasta ma ayyukan karfi, ko ake aura ba da amincewarsu ba, da wadanda ake tilasta ma yin karuwanci, da kuma wadanda ake safararsu, da wadanda aka sa cikin kangin bashi.

Rahoton ya bukaci kasashen duniya su kara hada karfi wajen yaki da dabi'ar, a kan kuma gwamnatoci su kara tsananin hukunci kan masu safarar jama'a.