Boko Haram: Adamawa za ta bai wa 'yan banga aiki

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan banga na taka muhimmiyar rawa a yakin da ake yi da Boko Haram

Gwamnatin jihar Adamawa a Nigeria ta ce za ta yi dauki 'yan banga da mafarauta aiki domin su taimaka wa sojoji wajen yaki da Boko Haram.

Gwamnatin ta ce ta kafa wani kwamiti da zai bayar da shawara a kan yawan mutanen da za a dauka aikin da kuma albashin da ya kamata a rika ba su.

Da ma dai wasu manyan 'yan arewacin kasar irin su mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da mataimakin shugaban kasar, Atiku Abubakar sun yi kira da a kafa kungiyoyin 'yan banga domin tunkarar 'yan Boko Haram.

A 'yan kwanakin nan dai ana ci gaba da dauki-ba-dadi tsakanin 'yan kungiyar Boko Haram da sojojin Nigeria a jihar ta Adawama, abin da ya kai ga 'yan kungiyar kwace wasu garuruwa.

Karin bayani