An rantsar da shugaban riko a Burkina Faso

Hakkin mallakar hoto none
Image caption Michel Kafando tsohon ministan harkokin wajen Burkina Faso ne

Shugaban rikon kwarya na kasar Burkina Faso, Michel Kafando ya yi rantsuwar kama aiki a wani biki da aka gudanar a Ouagadougou, babban birnin kasar.

Daga cikin wadanda suka shaida rantsuwar kama aikin, sun hada da alkalan kotun tsarin mulki, da manyan hafsoshin soji, ciki har da jagoran mulkin sojan kasar na wucin gadi mai barin gado, Laftanal Kanar Isaac Zida, da sauran jama'a.

Shugaban kotun tsarin mulkin kasar ta Burkina Faso, Albert Millogo, ne ya rantsar da shi.

Zaben shugaban rikon kwaryar ya biyo bayan zanga-zangar hambarar da gwamnatin Blaise Compaore da kuma boren neman soji su mika mulki ga farar hula.