Jama'iyar APC ta yi zanga zanga a Abuja

Sulaiman Abba, Sufeta Janar na Yansandan Najeriya Hakkin mallakar hoto Nigeria Police
Image caption Sulaiman Abba, Sufeta Janar na Yansandan Najeriya

Jiga-jigan jam'iyyar adawa ta APC a Najeriya sun yi wata zanga-zanga a Abuja don bayyyana wasu korafe-korafensu, ciki har batun tsawaita dokar ta-baci a jihohin Borno da Yobe da Adamawa.

Tsohon shugaban Najeriya Janar Muhammadu Buhari mai ritaya da wasu gwamnoni na daga cikin wadanda suka halartaci zanga-zangar, inda suka yi tattaki har hedikwatar 'yan sandan kasar.

Wani korafin da 'yan jamai'iyar da APC suka gabatar ga Sufeta Janar na Yansandan Najeriya shi ne cewar jama'iyar da ke mulki na neman yin amfani da 'yansandan a matsayin na jama'iyar.