Dokar ta-baci : Kan majalisa ya rabu

Hakkin mallakar hoto davidmark facebook
Image caption A ranar Alhamis ne wa'adin dokar na watanni shida-shida a karo na uku zai kare.

A ranar Larabar nan ne 'yan majalisar dattawan Najeriya za su ci gaba da tattauna bukatar shugaban kasar ta son tsawaita dokar ta-baci a jihohin kasar uku da ke fama da rikicin Boko Haram, lamarin da ya raba kan 'yan majalisar.

Tun ranar Talata ne 'yan majalisar suka soma mahawara kan bukatar tsawaita dokar a karo na hudu a jihohin na Borno da Yobe da Adamawa.

An samu rabuwar kai tsakanin 'yan majalisar akan wannan batu bayan da wasu suka lashi takobin cewa ba za su amince da bukatar ba.

Haka kuma a ranar Alhamis ne 'yan majalisar wakilan kasar za su katse hutun da suke yi su dawo su tattauna kan bukatar ta Shugaban kasar.