Haihuwar bakwaini na kara mutuwar yara

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Koshin lafiya kafin daukar ciki na daga abubuwan da ke hana haihuwar bakwaini

Wani bincike da likitoci a Burtaniya suka gudanar ya nuna cewa haihuwar jarirai bakwaini na kan gaba wajen haddasa mace-macen kananan yara a duniya.

Binciken wanda mujallar nan ta kiwon lafiya mai suna Lancet ta wallafa, ya gano cewa akan samu mace-macen bakwaini fiye da miliyan daya a duk shekara, kuma lamarin ya fi kamari a yammacin Afrika.

Wata likita a Asibitin Malam Aminu Kano, Dr Zubaida Faruk ta ce, rashin lafiyar uwa na daga matsalolin da ke haddasa haihuwar bakwaini.

Rashin lafiyar da ya hada da zazzabin cizon sauro da ciwon sukari da hawan jini da tarin fuka da ciwon zuciya da fargaba ko tsoro, inda wasu daga ciki ke sa uwa ta shiga nakuda kafin lokaci.