Apple zai sa kidan Beats a wayoyinsa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Beats ya yi fice wajen yin na'urar sauraren sauti da ake sanya wa a ka.

Kamfanin Apple zai sanya manhajar kade-kaden kamfanin Beats a dukkanin wayoyinsa na iPhone da iPads.

Jaridar Financial Times ta ruwaito a shekara mai zuwa ne kamfanin na Amurka zai sanya sautin.

Rahoton ya ce, kamfanin na Apple zai sanya manhajar sautin na Beats(app) a sabbin samfuran iPhones da iPads da yayi na baya bayan nan.

Apple ya sayi kamfanin Beats, wanda aka fi sani a fannin kera na'urar sauraren sauti da ake sa wa a ka (headphones), akan dala biliyan uku a farkon shekarar nan a watan Mayu.

Da aka nemi jin ta bakin kamfanin na Apple game da wannan rahoto na jaridar ta Financila Times, ya ki cewa komai.

Hakkin mallakar hoto Getty

Wannan shiri na sanya sautin na Beats da Apple ke shirin yi zai jawo masa sabbin masu sayen kayansa.

Haka kuma shirin zai kawo barazana ga kaka-gidan da kamfanin Spotify ya yi a kasuwar wannan fanni.

Sai dai kuma mawaka suna korafi da cewa kudin da ake ba su na ladan sanya wakokinsu a manhajar wayoyi bai kai abin da ya kamata a ba su ba.

Wannan ne ma ya sa Taylor Swift fitar da kade-kadenta daga kamfanin Spotify.