Dokar ta-baci: majalisar wakilai za ta yi zama

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ranar Alhamis din nan ne dokar ta-bacin da aka sanya a jihohi uku za ta kare

A Nigeria, yau ne Majalisar wakilan kasar za ta katse hutun da ta ke yi don tattauna bukatar da shugaban kasar ya aike wa Majalisun dokokin kasar na neman tsawaita dokar-ta-baci a jihohin Borno da Yobe da Adamawa.

Majalisar wakilan dai za ta yi wannan zama ne yayin da a bangare guda 'yan majalisar dattawa a karo na biyu suka kasa cimma matsaya kan bukatar tsawaita dokar ta-bacin.

Su dai 'yan Majalisar dattawan sun ce za su ci gaba da muhawara a ranar Alhamis din nan ne bayan sun saurari bahasi daga manyan hafsoshin sojin kasar wadanda suka gayyata domin halartar zaman da za su yi a yau din.

Batun tsawaita dokar ta-bacin domin yaki da kungiyar Boko Haram, tuni ya raba kan 'yan majalisar dattawan, tsakanin masu goyon baya da masu adawa.