Boko Haram:Sanatoci sun tashi baram-baram

Hakkin mallakar hoto davidmark facebook
Image caption Shugaban majalisar dattijai, David Mark

A rana ta biyu a jere, 'yan majalisar dattijan Nigeria sun ta shi baram-baram a kan batun tsawaita dokar-ta-baci a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa.

Shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan ne ya bukaci 'yan majalisar su amince da bukatarsa ta tsawaita dokar ta-baci domin ci gaba da yaki da kungiyar Boko Haram.

Bayan kwashe kimanin sa'o'i uku suna muhawara a asirce, sanatocin sun kasa cimma matsaya kan batun.

Saboda sabanin, sanatocin sun dage zama har zuwa ranar Alhamis domin ci gaba da tattaunawa kan matsayin da za su dauka.

Har ila yau, 'yan majalisar dattijan sun yanke shawarar gayyatar manyan hafsoshin Nigeria su bayyana gabansu domin warware musu inda aka kwana game da yaki da Boko Haram.

Bayan kafa dokar ta-baci a watan Mayun 2013 ne, 'yan Boko Haram suka tsananta hare-hare inda a halin yanzu suka kafa totocinsu a garuruwa da dama a arewa maso gabashin kasar.