Za a gurfanar da Korea ta Arewa ICC

Shugaban Korea ta Arewa Kim Jong Un Hakkin mallakar hoto
Image caption A na cin zarafin bil'adama a Korea ta Arewa.

Kwamitin kare hakkin bil'adam na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da shawarar da ta bukaci kwamitin tsaro na Majalisar ya gabatar da batun mummunan take hakkin bil'adam da Korea ta Arewa ke yi ga kotun manyan laifuka ta duniya da ke Hague.

Rahoton da Kwamitin bincike na Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar a farkon wannan shekarar ya bayyana yadda ake take hakkin bil'adama aKorea ta kudun ta ta hanyar kuntatawa da cin zarafin mutane.

Haka kuma ya yi gargadin cewa ta yi wu shugaban Korea ta Kudu Kim Jong Un ya fuskanci takunkumi.

A makwannin da suke tafe ne kwamitin binciken na MDD zai kada kuri'a akan rahoton da ya gabatar wanda ba lallai ne a aiwatar da shi akan Korea ta kudun.

Rasha da China Wadanda suke da ikon hawan kujerar na ki, sun kada kuri'ar kin amincewa.