An rufe majalisar dokokin Nigeria

David Mark Hakkin mallakar hoto davidmark facebook

Shugaban majalisar dattawan Nigeria ya bada umarnin a rufe majalisar dokokin kasar ba tare da bata lokaci ba har sai zuwa makon gobe.

Hakan dai ya biyo bayan wata hayaniya ce da ta barke a majalisar a yau, bayan da jami'an tsaro suka hana Kakakin majalisar wakilai shiga harabar majalisar.

Kakakin majalisar, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal, wanda a cikin kwanakin nan ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP mai mulki zuwa jam'iyyar adawa ta APC ya je majalisar da niyyar jagorantar wani taro, amma jami'an tsaro suka hana shi shiga harabar majalisar.

Duk da cewa kakakin ya shaidawa jami'an tsaron cewa shine kakakin majalisar wakilai, amma wadanda suka ganewa idanunsu sunce jami'an sun yi mirsisi suka hana shi shiga majalisar

Kakakin majalisar da kanshi ya yi ta kiran jami'an da ke bakin kofa ba tare da sun amsa ba, inda suka rufe kofar majalisar.

Hayaniya dai ta barke tsakanin jami'an tsaro da tawagar kakakin majalisar wakilan, inda daga karshe aka bankare kofar majalisar domin kakakin ya shiga.

Yan sanda sun harba barkonon tsohuwa, wanda ya shafi dukkanin mutanen dake wurin ciki har da kakakin majalisar wakilan, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal.