Gudunmaya kan yaki da dimamar yanayi

Matsalar dumamar yanayi ta addabi kasashe matallauta Hakkin mallakar hoto AFP

Wasu kasashen duniya masu karfin tattalin arziki, sun yi alkawarin bayar da Dala biliyan 9.3 ga asusun dake kula da dumamar yanayi domin a taimakawa kasashe matallauta wajen yaki da dumamar yanayi.

Mafi yawan kudaden an same su ne gabanin fara taron Berlin, kuma hada kudin na daga cikin matakan da ake dauka wajen ganin a cimma matsaya guda a yakin da ake yi da canjin na yanayi inda ake sa ran nan da karshen shekara mai zuwa za a cimma yarjejeniya.

Majalisar Dinkin Duniya dai na sa ran za ta samu karin wasu alkawwura na dala biliyan goma, domin taimakawa kasashe marasa karfi wajen yin amfani da makamashin da ba ya gurbata muhalli.

Karin bayani