Mark ya ba da umurnin a rufe majalisa

Hakkin mallakar hoto davidmark facebook
Image caption Sanata David Mark

Shugaban Majalisar dattijan Nigeria, David Mark ya ba da umurnin rufe majalisar dokokin kasar sakamakon yinkurin da 'yan sanda suka yi na hana Shugaban majalisar wakilai shiga zauren majalisar.

'Yan sanda sun harba barkonon-tsohuwa ga Aminu Tambuwal da sauran 'yan majalisa amma daga bisa suka shiga cikin zauren majalisar da karfin tuwa.

Mr Mark ya ce an dage zaman majalissun biyu har sai ranar Talata domin kauce wa karya doka da oda.

A lokacin da Sanata Mark ya bada sanarwar, 'yan majalisar wakilai na ci gaba da zama a cikin zaurensu.

Hayaniya ta kaure ne a majalisar dokokin Nigeria bayan da 'yan sanda suka harba barkonon-tsohuwa domin hana shugaban majalisar wakilai, Aminu Waziri Tambuwal shiga cikin zauren majalisar.

Tun bayan da Aminu Tambuwal ya bar jam'iyyar PDP ya koma APC, gwamnatin tarayyar ta janye masa jami'an tsaron da ke kare lafiyarsa.