An harba wa 'yan majalisa barkonon tsohuwa

Hakkin mallakar hoto peoples daily
Image caption Bisa dukkan alamu akwai sauran tashin-tashina a majalisar

Hayaniya ta kaure a majalisar dokokin Nigeria bayan da 'yan sanda suka harba barkonon-tsohuwa domin hana shugaban majalisar wakilai, Aminu Waziri Tambuwal shiga cikin zauren majalisar.

Bayanai sun ce da karfin tuwo Tambuwal da wasu 'yan majalisar da ke rufa masa baya suka shiga cikin zauren majalisar.

Daga bisani shugaban majalisar dattijai, David Mark da wasu sanatoci sun shiga cikin zauren majalisar wakilai domin kwantar da kurar.

Tun bayan da Aminu Tambuwal ya bar jam'iyyar PDP ya koma APC, gwamnatin tarayyar ta janye masa jami'an tsaron da ke kare lafiyarsa.

Bayanai sun ce yanzu haka 'yan majalisar wakilan suna ta tattaunawa a tsakaninsu domin sanin matakin da za su dauka a nan gaba.