Niger ta tura jirage Mali don kai hari

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An tura jiragen ne domin kai wa wasu mahara farmaki

Jamhuriyyar Niger ta aike da jiragenta masu saukar ungulu kan iyakarta da Mali domin kai wa 'yan tawaye hare-hare bayan sun kai hari garin Bani-Bangou.

Garin na Bani-Bangou, wanda ke karkashin Jamhuriyyar ta Niger, yana kan iyakarta da Mali ta yankin yammaci.

Jami'an soji da mazauna garin sun tabbatarwa kamfanin dillacin labarai na Reuters cewa jiragen sun isa garin.

Mazauna garin sun ce a ranar Talata ne wasu mahara a cikin motocin a-kori-kura da babura suka suka kai hari a garin, kodayake sun yi ba-ta-kashi da jami'an tsaro kasar, lamarin da ya sa mutane suka rika guduwa.

Karin bayani