Kotun Koli ta cire gwamnan riko na Taraba

Image caption Jihar Taraba dai ta fada rikicin siyasa tun lokacin da gwamna Danbaba Suntai ya yi hatsarin jirgi

Kotun Kolin Nigeria, ta bayar da umarnin cire gwamna riko na jihar Taraba, Alhaji Garba Umar.

Kotun ta kuma yi umarni a rantsar da Alhaji Danladi Abubakar, tsohon mataimakin gwamnan jihar.

Wannan mataki ya faru ne bayan karar da Alhaji Abubakar ya kai cewa ba a bi ka'ida ba wajen cire shi daga mukaminsa a shekarar 2012.

'Yan majalisar jihar Taraba ne suka tsige shi daga mukaminsa a wancan lokacin, bayan da suka zarge shi da gudanar da harkokin kasuwanci.

Karin bayani