Amurka za ta tasa keyar wasu bakin haure

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Amurka zata kyale wasu bakin haure da suka cika ka'idoji cigaba da zama a kasar

Shugaba Obama na Amurka ya yi jawabi ga al'ummar kasar don zayyana sauye-sauyen da aka yi ma tsarin karbar baki.

Yace zai yi amfani da karfin ikon sa na bayar da damar zama cikin kasar ta wani takaitaccen lokaci ga wasu bakin-haure miliyan biyar.

Akasarinsu Iyayen Amurkawa ne da kuma mutanen dake da matsayin zama na dindindin wadanda ke zaune cikin kasar tun shekaru biyar da suka wuce.

Za a gaggauta tasa keyar sauran bakin-hauren.

Shugaba Obama ya ce Amurka ta ginu ne da hadin-gwiwar baki don haka bakin da suka zamo masu aiki ne tukuru suna bukatar samun karin dama.

Yace an yi sauye-sauye ga tsarin da ake amfani da shi a yanzu, tare da sukar lamirin 'yan jam'iyyar Republican saboda babbakewar da suka yi ta gudanar da sauye-sauyen.